011 HAUSA LAMAHAT MIN HAYATI SAID AL NURSI.indd

Transkript

011 HAUSA LAMAHAT MIN HAYATI SAID AL NURSI.indd
RASA’ILINNUR
SUNA KAN IDON
DUNIYA
SÖZLER PUBLICATIONS CAIRO BRANCH
30 Gafar Al Sadek St., Hay Al Sabi, Nasr City.
CAIRO / EGYPT
Phone/ Fax: +(202) 22 60 29 38
E mail: [email protected]
SÖZLER PUBLICATIONS MAIN BRANCH
S. Demirel Bulvari Aykosan San. Sitesi 4’lü
A Blok Kat: 3 No: 244 Ikitelli / Istanbul / Türkiye
Tel: +90 212 671 25 47 - 48 pbx
Tel: +90 212 527 10 10
Fax: +90 212 671 25 49
www.sozler.com.tr
NUR PUBLICATIONS
P.O. Box 15214
Scottsdale, AZ 85267-5214, USA.
Tel: 1-800-825 9027
Fax: (602) 493 9798
Islamische Gemeinschaft Jama`at-un Nur e.V.
Neustr. 11, 51063 Köln
Tel: (0221) 61 72 27
Fax: (0221) 61 10 375
www.jamatunnur.de
[email protected]
L
RASA’ILINNUR
SUNA KAN IDON DUNIYA
MAWALLAFI
BADI’UZZAMAN SA’ID ANNURSI
Lalle Rasa’ilunnur wasu qwararan hujjojine
game da Alqur’ani mai girma, da kuma bayani
kan matsayinsa. Rasailunnur wata walqiyace
mai haskawa daga cikin hasken Alqur’ani,
sannan wata kamfatace daga cikin koginsa
kuma wani haskene daga ranarsa, kuma wata
haqiqace daga taskar ilimin haqiqa, haka kuma
wata kwaranyace daga makwaranyarsa.
FASSARA ZUWA HAUSA
KABIR UTHMAN IMAM
AZARE.
8
5
Badi’uzzaman Sa’id Annursi ya rayu a
azamanin sarki (Abdulhamid na biyu), qarsheqarshen daular usmaniyya yayin da take dab da
faxuwa, kuma ya rayune cikin burin maqiya
da cincinrindonsu wajan ganin bayan wannan
daula, daliliko bayan sarki yayi murabus,
(Ittihadiyyun) sun kawo sarki (Muhammad
rashad), kana suka jefa daular usmaniyya cikin
yaqin duniya na farko, wanda hakan ya kai ga
shiga daular cikin mawuyacin hali, daga nan
(Ittihadiyyun) suka gudu suka bar al’umma
cikin girbin abin da wannan yaqi ya shuka,
bayan wannan yaqi yasa waxannan garuruwa
qarqashin tumurmusan sojojin haure, daga
nan sai sarki Muhammad Waheeduddeen yazo
bayan sojojin Ingila da yunan da Itali da Arman
sun mamaye wurare daban–daban a Toki, har
ma (Istanbul) da kanta ta kasance qarqashin
ikon Ingila, wato a wannan yanayi sarkima da
kansa ya kasance yana qarqashinsu.
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
SHIMFIXA
6
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
“Yan qasar Toki sun dawo basu da komai
banda imani mai qarfi wanda suke amfani da
shi wajan kare kansu daga cutar maqiya, kuma
suke amfani da shi wajan yaqan masu mulkin
mallaka, ana haka sai “yan qasa suka tattara
abinda ya ragemusu na kayan yaqi sukayi shirin
kutsawa yaqi da gaske dan faxama waxanda
suke yaqarsu, wanda ake qiran wannan yaqi
(Harbul istiqlal) wato yaqin neman yancin kai.
Sadai bayan abubuwa sun lafa, sai wata
baqar gaba ta bayyana, da kuma qoqarin
cisge imanin da ya sami gurbin zama azukatan
al’umma, acikin wannan yanayi mai firgitawa
da wannan al’umma ta sami kanta aciki,
Badi’uzzaman ya xauki azamar ceto wannan
imani , ya kuma sadaukar da kansa akan haka,
saboda ya sharewa al’ummarsa hawayensu, sai
ya duqufa kan rubuta (Rasa’ilunnur) kuma ya
watsasu cikin al’umar don tabbatar da cibiyar
musulunci cikakkiya,
HAIHUWARSA
An haifeshi a farkon qarni da ya shuxe a
shekara musulunci ta 1293ah wanda yazo dai –
dai da 1877ad a shekarar girigori, cikin garin
(Nors) dake kudu maso gabacin tokiya a yanzu,
iyayensa sun kasance masu kamun kai na buga
misali a wannan gari, sun samasa suna (Sa’id).
NEMAN ILIMINSA
7
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Take Sa’id ya shiga makarantun zaure da
tsangayun ilimi da suke wuraren gudumarsu,
gashi ya kasance yana haddace duk abin da yaji
na karatu, ba wuya ya zama zakaran gwajin
dafi a waxannan tsangayu, daga nan zamansa
a wannan gari yai karanci sakamakon tafiyetafiyen neman ilimi, daga wannan gari zuwa
wancan.
Bayan ya tattare abin da ke ga malumansa,
sai ya wayi gari yana xaukar ilimi acikin littafai
da kansa kamar abin da ya shafi Tafsiri, Hadisi,
Nahw, Tauhidi, Fiqhu, da Manxiq. Sannan ya
kasance abin buga misali wajan hadda, saboda
duk abin da ya gani da cikin waxannan ilmoma
ya kiyaye, a haka saida ya haddace littafai
casa’in (90) daga cikin littafan da ake ji dasu.
Ya samu damar tafka muhawara da maluma
tun yana qaraminsa, sakamakon tarun ilimi da
Allah ya bashi. Anyi tarurruka daban- daban
don ya kara da manyan maluma, kuma ya sami
nasara akansu, har ya sanu a duniya.
A shekara ta 1314ah/1897ad ya fantsama
garin (wan) ya duqufa kan karanta littafan
Riyada , Falaki , Kimiyya , Jiyoloji , Falsafa ,
dakuma sauran wasu vangarori , daga nan ake
kiransa da badi’uzzaman; saboda tsagogaran
iliminsa da kaifin qwaqwalwar sa haxi da
yawan bincike.
LABARIN DA YA HANASHI SUKUNI
8
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Awannan tsakankani aka watsa cikin takardu
cewa ministan masu mulkin mallaka (Gladson)
ya bayyanawa “yan majalisa burtniya cewa:
“da zarar qur’ani yana hannun musulmai bazai
tava yiwuwa su dawo qarqashinmu ba, sabo da
haka ba makawar sai munkawar dashi a bayan
qasa ko mun raba su da shi”. Wannan labari ya
jijjigashi ya hanashi rintsawa daganan sai ya
tabbatarwa mutanensa: “sai na tabbatrwa duniya
cewa qur’ani wata ranace wacce haskenta
baya disashewa ko ya gushe”. Daganan ya
nufi (Istanbul) a shekara ta 1325ah/1907ad ya
gabatarwa sarki (Abdulhamid na biyu) qudurin
kafa wata tsangaya ko jami’ar islama a kudancir
(Adanul) ya samata suna (madarasatuz zahara)
bisa tsarin azhar, don yaxa haqiqanin muslunci
sannan kuma ta gwama ilimin addini da na
zamani kamar yadda yake cawa: “ilimin
addini shine hasken zuciya, hasken hankali
shine ilimin zamani saboda haqiqa na cikin
hadakarsu, rabasu kuma shine “yan ubanci”.
A shekara ta 1329ah/1911ad yayi bulaguro
zuwa (sham) kuma ya haxu da manyan
malumanta, sukayi shiru suna sauraran
kuxubarsa a masallacin bani umayya cikin
dubban muatane sabida tsantsan iliminsa da
suka fuskanta , wacce wannan kuxubar ana
qirgata da cikin taskokin da ya bari, ana mata
9
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
take da (Al-kuxbatisshamiyya) kuma wannan
kuxubar tana xaya daga cikin waxanda sukayi
cikakken bayani kan siyasa da zamantakewa.
JARUMTARSA A GABAN KOTUN SOJI
Badi’uzzaman sa’id annaursi yana xaya
daga cikin waxanda aka gurfanar a gaban
kotu gaban itatuwan rataya a qarshen rikicin
31maris, saboda ansan irin gudummawar
dayake bayarwa tadaidata al’mura, tunda ya
kasance yanawa sojoji nasiha da sukoma subi
umarnin manyansu…
Bayan haka yayiwa waxannan sojoji kuxuba
kan wannan manufa qwarai da gaske.
Ana cikin wannan rikicin ya tabbatarwa
kotu cewa: “lalle ni xalibin shari’ane, sabo
da haka nake auna kowane abu da ma’aunin
shari’a, kuma muslunci nasa a gaba, don haka
nake daidaita komai nake dubansa da madubin
muslunci.
Lalle ni ko dayake ina kurkuku ina tsimayar
rataya bazangusheba ina tsokaci akan abin
da yake gudana a al’umma na daga zalunci
da kama-karya, to bayanina ba’da ku kadai
nake yiba, har dama kowa dakowa a wannan
zamani, don gaskiya ta bayyana qarara daga
kwarmin zuciya karkashin sirrin wannan aya
﴾ J I H ﴿ amma wanda yake baarene
bazai ganeba, ni na shiryawa zuwa lahira,
kamar yadda waxannan ratayayyu suka tafi.
10
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Haqiqa wannan gwamnati tana aadawa
da hankali, sai dai yanzu gabar takai har kan
rayuwa gaba xaya. Idan hukuma ta kasance
akan irin wannan tsari kuwa to hauka ta sami
gurbin zama. Wutar jahimu kuma ta tabbata ga
azzalumai.
Dama na kasance ina burin tanadin wani
wuri da zan baje kolina sai gashi Allah yasa
wannan kotu tazamo wurin da yafi cancanta da
yaxa manufata.
A farkon lamari sun tambayeni kamar
yadda aka tambayi sauran cewa kanason
shari’a?! nace: “da ace inada rai qwaya dubu
zan sadaukar da su akan haqiqa guda daya daga
cikin haqqin shari’a, tunda dai shari’a itace
jigon dacewa, kuma itace adalci tsantsa sannan
itace daukaka, ina nufin shari’ar gaskiya ba ta
qaryaba.
Ana cikin haka sai hukuncin kuvutar
Badi’uzzaman daga wannan kotu da take rataye
mutane ya sauka.
ANNURSI A MATSAYIN JAGORA
KUMA MAI TAFSIRI
Ba abin mamakibane ya kasance daga cikin
mayaqa a lokacin da yaqin duniya ya varke,
Badi’uzzaman ya shirya runduna daga cikin
xalibansa don taran aradu da ka wajan kare
qasa. Ya samu rauni a haxuwarsa da rundunar
(rus) suka damqeshi rai a hannun Allah har
11
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
zuwa (qwastorma) ta wuraren rasha inda ya
shafe shekara biyu da wata huxu, har Allah ya
kuvutar da shi yayin (zaga-zangar balshafiya),
take ya dawo qasarsa, kalifa shaikul islam, da
babban jagora da sauran xaliban ilimin shari’a
sun kyautata tarvarsa, kuma aka bashi lambar
yabo. Sannnan daular usmaniyya ta xoramasa
nauyin ruqe wasu muqamai shi kuma yaqi , har
sai da aka bashi jagorancin sojoji xaya daga
cikin kujerun (Darul hikmatil islamiyya) wanda
ba’a bawa kowa sai xaya daga cikin manyan
maluma. Daga nanne ya yaxa mafiya yawan
rubuce-rubucen sa da yayi a cikin yaren larabci,
acikinsu akwai tafsirinsa mai suna:(Isahratul
I’ijaz fi mazaannil iijaaz) wanda ya rubutashi
acikin ruguntsimin yaqe-yaqe, da kuma
littafinsa (Almasnawee al-arabi annuri)
HARBI A MAKASA
Bayan mayaqa sun shiga (Istanbul)
annursi yaji cewa akwai wani zagon qasa
da duniyar musulunci take fuskanta. Sai
yakasance yazama dole yatsaya daga cikin
dakarun da zasuyi fito nafito da kama karya
dakuma dakusarwa.sai ya gaggauta kyautata
wani dan littafi(ALKHADAWATUSSIT)
wanda yamotsa himmar yan kasa dashi,kuma
yasanya tunaninsa kan kauda qasqanci da yaye
abubuwan dasukesa daular uthmaniyya yanke
kauna sakamakon rikice-rikice.
12
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
MAWUYACIN HALI
A wannan lokaci wato tun (1922ad) aka
sauke wasu dokoki don cisge musulunci tun
daga qarqashinsa, dakuma kashe haskensa
cikin zuciyoyin al’ummah bayan wannan shiya
daga tutan musulunci tsawon karni shida, daga
nanne akayi watsi da ikon daular ranar1/11/1922
sannan watsi da khalifanci ya biyo baya. Uku ga
watan ukune 3/3/1924 aka hana koyar da addini
a makarantu gaba daya, sai aka canja lambobi
daga harshen larabci zuwa yaren latin, aka hana
kiran sallah da yin sallah cikin yaren larabci,
akayi kokarin fassara qur’ani acikin ayyukan
bauta sannan aka hana duk wani kokari da zai
kawo ci gaban musulinci tunda aka hana buga
litattafan musulinci.
Sai aka tilasta mutane wajen canja shigarsu
zuwa shigan turawa maza su sanya (hana
sallah) kaboyi, mata kuma na fidda tsaraici.
Daga nan suka kafa hukumomi waxanda
suka dasa tsoro da firgici a faxin gari, sannan
suka kafa itatuwan rataya ga manya manyan
maluma, da kuma waxanda zuciyoyinsu suke
raya musu juyawa gwamnatin baya, sai tsoro
da firgici ya game garin, har saida abin yakai
ga cewa mutane suna voye qur’ani don kada
ma’aikatan gwamnati su gani, sai aikin jarida
yasami karfin gwuiwa wajen yada munanan
xabi’u da izgilanci a addini, ta hakane litattafan
marasa addini suka sami yaxuwa.
13
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
KAXAITA AL’QIBLA A CIKIN
AL’QUR’ANI
Ustaz nursi yana siffanta halin ruhinsa da
juyawan tunaninsa bisa abubuwa masu zuwa;
Sa’eed yasha duka mai raxaxi “ acikin
shekaru talatin da suka gabata Saee’d yasha
gwa gwar maya da wahal-halu iri-iri sakamakon
samun kansa da yayi cikin rafkana da ximuwa,
amma yanzu yayi tunani cikin lamarin, cewa
mutuwa gaskiyace sannan yasamu kansa cikin
tar-naqaqi sai ya nemi mafita, daga nanne
yanemi wanda zai kama hannunsa… saiya
ximauce yayinda yaga hanyoyi sun rarraba a
gabansa, take ya xauki littafin futuhul’gaib, naSheikh Abdul’qadir Al’jilani ya buxeshi yana
mai fatan dacewa, sai yaci karo da wannan
bayani mai zuwa “ yanzu kana (darul’hikma)
kanemi likitanda zai magance zuciyarka…
abin mamaki wata rana na kasance cikin wani
bangare daga cikin darul’ hikimah na musulinci,
sai yazamo kamar najene don magance ciwukan
al’ummar musulmi saidai kuma ciwona yafi
na kowa, kuma nafi kowa buqatuwa zuwa ga
magani, to! Abinda yafi ga kowane mara lafiya
yamagance kansa kafin yamagance waninsa.
Qwarai, kai baka da lafiya kanemi likita ya
dubaka, haka malam yafaxamin, nace;- malam
kazama likitana mana! Sai nafara karanta
wannan littafi naji kamar dani yake Magana,
ya kasance mai kakkausan lafazi wajen kauda
14
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
ruxin zuciyata, take ya gudanarda bincike mai
zurfi a cikin zuciyata… ban jureba… saboda na
lura cewa bayaninsa ni kawai yake fuskantowa
dashi.
Qwarai, haka na karanta kusan rabin littafin
amma na kasa qarasawa… sai na azashi a
wajenda yake, daga baya sai naji a jikina cewa
raxaxin wannan ciwo ya kau, sai wani daxi da
annashiwa na ban mamaki ya maye gurbinsa…
na koma zuwaga littafin naqarasa karantashi,
kuma na qara da abubuwa da dama, kuma naci
gaba tare dashi.
Lokaci mai tsawo ina sauraran kyawawan
wurude-wurudensa, da kuma qawatattun
ibadunsa, sannan nasami littafin (maktuubat)
na Imam Ahmad Al’faruqee, Al’sarhandi, nayi
kwadayin samin al’khairi acikinsa, na buxeshi
sai naga abin mamaki… yayin da naga lafazin
(mai zara Badi’uzzaman) cikin daya daga
wasiqunsa sai naji kamar yana ambatan sunana,
saboda sunan mahaifina( mai zara) kuma dukkan
wasiqu guda biyun yana mai fuskantar dasu
zuwa (mai zara Badiuzzaman). Sai nace ; tsarki
ya tabbata ga Allah maxau kakin sarki, lallai
wannan yanamin maganane kai tsaye saboda
tsohon laqabin sa’eed shine (Badi’uzzaman),
duk da yake ban san wani da yasanu da wannan
laqabiba banda (Al’hamdani) da ya rayu aqarni
15
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
na hudu bayan hijra, to amma babu makawa
cewa akwai wani wanda bashiba, wanda ya
rayu da imam (Al’sarhandi) masanin Allah
kuma ake masa laqabi da wannan suna, sannan
kuma babu makawa cewa halinsa yana kama
da nawa har nakai ga samin maganin cutana a
cikin waxannan wasiqu(,Al’imam Al’sarhandi)
yana qarfafa wasiyya cikin waxannan wasiqu
dama wasunsu cewa a kaxaita al’qibla wato abi
limami mai shiryarwa guda xaya kada a shgalta
da waninsa.
A wannan lokaci wannan wasiyya bata dace
da irin tsarina ba da kuma abubuwan da suka
shafi ruhina ba… sai nafara tunani gadan-gadan
shin wane zanbi a cikinsu!bayanin wannan
zanbi koko na wancan!, nayi matuqan ruxewa
saboda ko wane yanada nashi abubuwanda
ya kevanta dasu, dakuma jan hankali, adalilin
hakane raina yakasa karkata kan xaya daga
cikinsu, a lokacinda narasa yadda zanyi cikin
matsananciyar rikita, kwatsam sai wani tunani
ya faxo mini daga Allah maxaukaki yana cewa:
lalle farkon xariqu da mavuvvugar waxannan
koguna da ranar waxannan taurari shine
Alqur’ani mai girma to don haka kaxaita alqibla
na haqiqa baya yiwuwa sai a cikin Alqur’ani,
to Alqur’ani shine mafi girman jagora… kuma
malami mafi tsarki… tun daga wannan rana na
16
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
rungumi Alqur’ani na riqeshi hanu bibbiyu,
kuma nake ciro komai daga cikinsa, koda yake
tanadina yagaza wajan bani damar kwankwaxan
madadin wannan magaskacin jarora, wanda
yake kamar “salsabil” (wani idon ruwane a
aljanna), amma da albarkar wannan littafi zamu
nuna falalarsa ga ma’abota zuciya,kowa dai-dai
da matsayinsa, to waxannan haskakan kalmomi
da aka ciro da Alqur’ani wato (Rasa’ilunnur) ba
mas’alolin ilimi da hankaline kawaiba harma
da abin da ya shafi zukata da ruhi, da kuma
halayen da imani yake samun kansa aciki, to
don waxannan mas’aloli sunanan kamar a
matsayin wasu ilmomine na Allah masu tsada
maxaukaka.
Wasu tashin tashina da tarzoma sun auku a
vangaren jagoranci, wanda Badi’uzzaman bai
kuvuta daga sharrin waxannan rigingimuba, take
aka koreshi shi da waxansu mutane masu yawa
zuwa yammaci (andal) cikin hunturu a shekara
ta 1926 A.D. sannan aka koreshi shi kaxai zuwa
wani tsibri mai nisa wanda ake kira (Barla).
FITOWR RASA’ILUNNUR
Al’ustz annursi yana bayyana yaya
Rasa’ilunnur suka bayyana da cewa:
“…na sadaukar da lokacina da qoqarina
na tsaya tsayin daka na mai da hankali kan
17
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
ma’anonin Alqur’ani mai girma da lura cikinsu,
sai na fara sabuwar rayuwa, bayan da qaddara
ta xaukoni daga wani gari zuwa wani, acikin
wannan yanayi wasu ma’anoni maxaukaka
suka kimsu cikin zuciyata, niko nakewa
waxanda suke tare dani shiftarsu, nake kiransu
da (Rasa’ilunnur), wato saqonnin haske. Lalle
waxannan saqonni sun samune daga hasken
Alqur’ani, hakanan na roqi Allah albarkaci
duk wanda ya rubutasu. Sabo da ina da yaqinin
cewa bawata hanya da zata kai ga tsare imanin
mutane in ba waxannanba. Hakanan mutane su
ka cigaba da wankansu suna yaxawa, wannan
shi yasa na sami yaqinin cewa wannan nufin
Allah ne don kiyaye imanin musulmai… sai
naga ya zama dole na qarfafa gwiwar duk wani
wanda yake himdimtuwa ta wannan hanya,
kamar yadda wannan addaini yayi umarni…”
Hakanan ya ci gaba da wallafa Rasa’ilunnur
har zuwa shekara ta 1950ad duk da yake ana
caccanzamasa kurkuku daga wannan kotu zuwa
waccan, har tsawon shekara ashrin da biyar,
amma haka baisa ya dakata daga rubuce-rubuce
da isar da saqonsaba, har saida Rasa’ilunnur
suka kai (130), bayan haka aka tattarasu aka
musu suna da (Kulliyatu Rasa’ilunnur). Allah
kuma baisa an fara bugasuba sai bayan shekara
ta 1954ad.
18
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
QAURA
Al-Ustaz Nursi ya amsa qiran Allah ranar
25/Ramadan/1960, an masa qabari abirnin
(Urfa), saidai sojojin da suke mulki a wannan
zamani basu barshi ya hutaba har a qabarinsa,
don kuwa sun toneshi bayan wata huxu da
busneshi, suka tattare qasusuwansa a jirgi zuwa
wani waje da ba wanda ya sani har ya zuwa
yanzu.
Allah ya jiqanshi da rahama ya kuma sashi
a aljanna.
19
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
MENENE RASA’ILUNNUR?
Al-Ustaz Nursi ya bayyana ma’anar
Rasa’ilunnur da cewa:
“Rasa’ilunnur wasu hujjojine karfafa game
da qur’ani, kuma suna dauke da gamsasshen
bayani kan matsayinsa, Rasa’ilunnur wata
walqiyace mai walqawa cikin haskensa
maxaukaki , kuma wata kamfatace daga cikin
koginsa, sannan wani haskene daga ranarsa,
kuma wata haqiqace ta gaskiya, haka kuma wata
kwaranyace daga kwaranyar ma’anoninsa…”
Rasa’ilunnur ba wai xariqun sufancibane,
amma su wata haqiqace ta haske wanda yake
kwaranya daga ayoyin Alqur’ani, ba kuma
an samosu daga ilimin gabacin duniyane ko
yammacin taba, amma su waxansu mu’ujizozine
na Alqur’ani da da Allah ya kevance wannan
zamni dasu.
Duka-duka Rasa’ilunnur dai fassarar
ma’anonin Alqur’anine wanda suke magance
matsalolin xan adam.
Tunda dai suna samar da tabbataccen imani
wanda yake rushe munanan quduri da hanyoyi
marasa kyau. Rasa’ilunnur suna bayanine kan
ma’anar tauhidi da kuma hujjoji kan haka.
Sannan suna yanke shakku kan aukuwar tashin
alqiyama, gaskiyar annabta, da kuma adalcin
shari’a da sauran makamantansu.
20
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Mafi girman al’amari shine bincike kan
abin da ya shafi kira zuwa ga Allah da soyayyar
ma’aiki, da kuma kwaxayin lahira, da abin da ya
shafi al’umm tare da siyasarsu, akan wannanne
ustaz nursi yake cewa: “lalle Rasa’ilunnur sun
shafi sirrukan addini, shari’a da kuma alqurani
tare da bayyanasu dalla-dalla, sannan kuma
suna yiwa kafirai da masu yiwa musulunci
zagon qasa linzami. Rasa’ilunnur sun ratsa
abin da ya shafi (mi’iraji) wato tafiyar Annabi
(s.a.w) zuwa sama, da abin da ya shafi tada
jikin xan adam ran tashin alqiyama, bayan haka
Rasa’ilunnur sun tabbatarwa ma’abota falsafa
wawtarsu har sai da waxansunsu suka shiga
cikin addinin Islama, bamakawa sai komai a
duniya ya dawo yanada alaqa da Rasa’ilunnur,
kuma ba laifibane ace Rasa’ilunnur wata
haqiqace ta Alqur’ani wacce take dacewa da
kowane zamani.
FAHIMTAR TSARIN ALQUR’ANI
Saboda bayanin bambamci tsakanin salon
Rasa’ilunnur da sauran rubuce- rubuce kan
abin da ya shafi sanin Allah da kuma imani na
haqiqa zamu gabatar da wannan bayani mai
zuwa:
“…lalle sanin Allah da ake cirowa daga
cikin ilimin tauhidi ba cikakken sanibane,
kuma bayasa zuciya ta natsu, amma a lokacin
da wannan sani ya haxu da tsari Alqur’ani
yana wayan gari cikakke ya kuma sa zuciya
‫ﺗﺪل ﺒﻟ أﻧﻪ واﺣﺪ‬
‫ء آﻳﺔ‬
‫و ﻞﻛ‬
Ma’ana
Cikin kowane abu akwai alamar da take
nuna kaxaitaka Allah.
Imani baya samuwa da ilimi kawai, saboda
akwai abubuwa da dama a cikin imani da
kowanne yana da buqatar xaukar rabonsa,
kamar yadda idan abinci ya shiga cikin jiki
yana rarrabuwa zuwa gavovi daban-daban
kowace gava dai dai da buqatarta. To hakanan
mas’alolin imani da za’a ambata anan gaba,
idan suka shiga cikin hankali da fahimta kowane
vangare dake ciki kamar : ruhi , zuciya, sirri,
rai da sauransu na xaukar kasonsa daidai da
shi, amma idan abincin wani vangare bai sami
shigaba to wannan vangare zai sami tawaya da
yankewar baya, kuma ya tabbata cikin rashin
wannan rabo.
21
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
ta samu natsauwa. Muna roqon Allah da ya
sanya kowane vangare daga cikin vangarori
Rasa’ilunnur wata fitilar Alqur’anice mai
haskawa. To kamar yadda sanin Allah wanda
yake daga ilimin tauhidi kaxai yake da tawaya,
to haka wanda yake daga sufancima kaxai. Idan
an auna da hanyar da take daga Alqur’anice kai
tsaye. Tsarin Alqur’ani shine yake vuvvugar
da ruwa zuwa kowane sashe cikin sauqi, don
kowace aya aka tava zuba take kamar sandar
annabi musa.
Dubi wannan maganar:
22
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
HANYOYIN YAXA RASA’ILUNNUR
Allah cikin ikonsa ya nufi malam(Ihsan
Qasim Assalihi) da ya fassara Rasa’ilunnur gaba
xayansu zuwa yaren larabci, cikin mujalladi
tara, mujalladi na goma kuma ya tattara abin
dake cikin taran. An buga waxannan littafai a
Istanbul da Alqahira.
Hakanan Allah ya nufi “yar uwa (Shukran
Wahida) da fassara “Alkalimat”, “Almaktubat”,
Asshu’aa’at” , da “Isharatul I’ijaz fi Mazannil
Iijaaz” daga cikin Rasa’ilunnur, kamar yadda ta
wallafa littafi guda kan tarihin rayuwar Ustaz
Nursi. Wannan bayan qananan saqonni da
yawa da ta fassarane.
Fassara ta cigaba da havaka a lokacin da
aka fassara Rasa’ilunnur zuwa yaren Almaniya,
Faransa, Rasha, Sifen, Faris, Kurdi, Malawi,
Cena, Bosina da sauran wasu yarurrukan ashiya
ta tsakiya da waxansu yarurruka daban.
Sakamakon waxannan saqonni da aka
fassara aka fara manyan tarurruka na ilimi
a jami’o’i daban-daban a sassan duniyar
musulunci, musamman qasashen Larabawa,
kamar:- Jodan, Misra, Aljeriya, Maroko, Yamen,
Maleshiya, Indunisiya, Bosna, Ostreliya, Ingila
da Amurka da sauransu.
23
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
TAQAI TACCEN BAYANI KAN ABIN
DA RAS’ILUNNUR GABAXAYA SUKA
QUNSA
Mawallafi: Badi’uzzaman Sa’id Annursi.
Wanda ya fassara zuwa larabci: Ihsan Qasim
Assalihi.
Rasa’ilunnur da Badi’uzzaman Sa’id
Annursi ya wallafa suna qunshe da vangarori
guda tara, wanda ya zuba abin da Allah
yasanar dashi daga hasken Alqur’ani da kuma
ma’anonin imani, sannan yayi shiftarsu ga
masoyansa duk da halin quncin da suke ciki,
yayi hakane da niyyar ceto imanin rayuka,
hankula dakuma ruhika, cikin ikon Allah ya
sanyawa “yan wannan zaman tsaftatacciyar
mashaya dag Alqur’ani; don kare adddini da
imani, da kuma tsarkake zuciya da hankali daga
munan abubauwa. Allah ya nufeni –duk da
gazawata-dana fassara Rasa’ilunnur gaba xaya
zuwa harshen larabci. Sune kamar haka:Mujalladi Na Farko: “Alkalimat”
Wannan ya qunshi saqonni guda talatin
da uku (33) wasu daga ciki suna bayani kan
(ibada) wato bauta da (aqida) wato qudri.
Sannan suna bayani kan irin kallon da mumini
kewa duniya, da kuma aikin xan adam, sannan
suna bayani kan cewa ribar kasuwancin bawa
24
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
na daga saida kansa da dukiyarsa ga ga Allah
maxaukaki. Kamar yadda suke bayani kan
cewa imani da Allah da ranar qarshe yana
warware qullin rayuwa, hakanan suna bayani
kan hikmar lokutan salla. Sai kuma wasiqa
mai cin gashin kanta wacce take bayani kan
tashin alqiyama qarqashin sirrin sunayen Allah
kyawawa, sai muhimmancin mutum a rayuwa,
haxa da awu tsakanin hikmar Alqur’ani da
falsafa. Sai bayani kan haqiqar sirrin Alqur’ani
a cikin halittu; sabo da taimkawa zukatan da
sallamawa yai musu qaranci, sai bayani kan
ma’anar jifan shexan, da gamsasshen bayani
kan kaxaitar zati Allah maxaukaki tare da
jimillar aikinsa, da kuma yadda yake halitta
adunqule da yanda yakeyi daban-daban, da
kuma bayanin kusancinsa zuwa garemu da
nisansa daga garemu, daku alaqar sunasa
“Alqahiru”, da “Arrahmanu”, sannan sai
bayani kan asalin abu mai kyau, sai bayani kan
tabbat da annabtar annabi Muhammad (s.a.w),
da bayani kan muhimmacin mu’ujizozin
annabawa wajan kwaxaitar da mutum kan
cigaba a neman ilimi, da kuma faxakar da
ran da yake wasa da salla, tare da bayani kan
rabe-raben waswasi da hanyoyin magancisu,
sai bayanin kaxaita Allah tare da gamsasshen
misali, da kumabyanain cikar mutum da imani
25
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
da kuma bayanin tajallin kyawawan sunaye bisa
duniya, da bayanin cewa zikiri shine mabuxin
sirruka da dama a rayuwa, sannan ya gabatar
da hayoyi goma shabiyu qwarara wajen gano
ingantaccen hadisi, da kuma bayani kan raberaben halitu, bayan haka akwai wasiqa da take
bayinin kasancewar Alqur’ani gagara badaune,
sannan wata wasiqar kuma na bayani kan ikon
Allah, da gwalgwadon da bawa yake da damar
zabi, sai wasiqar da take bayani kan abin da
aljanna ta qunsa, da bayani kan wanzuwar ruhi
da mala’iku,da dadilan tashi alqiyama, sannan
bayani kan mutumtaka “ni” da kuma sirrin
motsin qwayar zarra da aikinta, da hikimar
mi’irajin annabi da amfaninsa, da bayani kan
wata matsaya mai girma kan tauhidi, da kma
bi a sannu wajan gano ma’anonin sunayen
Allah tsarkaka. Amma wasiqar qarshe tana da
bagarori guda 33 wanda gaba xaya sun dubane
kan tauhidi.
An xanfara risaltullawami’I da a qarshen
wannan littafi waxanda suke kunshe da
waqoqin imani waxanda xalibai sukayi.
Mujalladi Na Biyu: Almaktubat
Wannan shima ya qunshi saqonni talatin
da uku, kuma yana farawane da amsoshin
tambayoyi kan rayuwar Kidr a.s, da kuma
bayani kan hikimar mutuwa ta kasancewarta
abin halitta, sai bayani kan wutar jahannama,
26
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
daga nan sai bayani akan rayuwar mawallafin,
da kuma irin lurarsa cikin duniyar halittu,
da kuma wajabcin bawa mas’alolin imani
muhimmanci a wannan zamani, sai bayani kan
hikimar auren ma’aiki s.a.w da sayyida zainab
Allah ya qara mat yarda. Sannan sai bambanci
tsakanin karama da karramawa da “istidraji”
wato xaga qafa ko zuru da ido, kuma yadda
yake kasancewa a xabi’a, daga nan sai bayani
kan bambanci tsakanin imani da musulunci da
bayanin adalcin shari’a cikin rabon gado, da
hikimar fitar da Annabi Adamu daga Aljanna,
da hikimar halittar shaixanu da ashararai sai
bayani kan matsayar mawallafin game da
siyasa da dalilin da yasa ya nesanta daga ita,
dakuma hikimar dake cikin savani tsakanin
sahabbai Allah ya qara masu yarda, da kuma
bayani kan sauqar Annabi Isa tsira da aminci
su tabbata a gareshi, da kuma nuni kan cewa
tafarkin sahabbai da ma’abota faxaka shine
yafi. Sanna sai saqo mai cin gashin kansa cikin
mu’ujizozin annabi (s.a.w) yana xauke da
kimanin mu’jizozi guda xari uku waxanda aka
dogara da ingantattun hadisa wajan fiddasu, sai
kuma gamsasshen bayani kan imani da Allah
saninsa da soyayyarsa, da kuma hanyoyin kula
da iyaye da tsofaffi. Bayan haka sai wata wasiqa
27
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
mai cin gashin kanta, wacce take qunshe da
bayani kan “yan uwantaka tsakanin muminai
da hanyoyin magance savani, sai kuma
gamsasshen bayani kan abin da yake gudana a
duniya, na kashe-kashe da sauran masifu, sai
bayani kan abinda ya danganci sunan Allah
“Arrahmanu”, Ahakimu”, Alwadudu”, sannan
sai bayani kan sirrin addu’a da rabe-rabenta. Sai
kuma wasiqa da take wargaza maqarqashiyar
shexan game da Alqur’ani, da kuma cutar da
take tattare cikin kira zuwa wani vangaranci,
sai bayani kan madai dai ciyar hanya kan
savani cikin hanyoyin waliyyai, sai bayani
hanyoyin isar da saqon Rasa’ilunnur, sai bayani
kan godiya da amfaninta, sai wata wasiqa
mai xauke da amsoshin wasu tambayoyi kan
mu’ujizar alqurani da kuma sanin haqiqarsa.
Bayan wannan sai wasiqa ta musamman kan
hikimar azumi, da kuma faxakar da mahaddata
Alqur’ani kan sharrin shaixanu, sai kuma
maida martini kan “yan bid”a da suke qoqarin
canza alamomin musulunci, daga qarshe kuma
sai wasiqa akan sufanci hagu da dama.
Sannan an xanfara wannan mujalladi
(nuwal haqa’iq), wato wata wasiqace da take
qunshe da gudummawar zuciyar mawallafi
Rasa’ilunnur.
28
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Mujalladi Na Uku: Allama’at
Wannan shima yana xauke da wasiqu
33, waxanda suke farawa da bayani game da
abinda ya shafi rayuwar yau da kullum, kamar
yadda suke bayani kan munajatin annabi yunus
da Annabi Ayyuba amincin Allah ya tabbata a
garesu, sannan sai bayani kan matakan sunnar
Annabi (S.A.W), sai bayani kan hikimar neman
tsari daga shexan, sai bayani kan ilimin Allah
gami da tsokaci kan muhimmancin tattali da
gujewa almubazzaranci, bayan haka sai wasiqu
guda biyu kan gundarin iklasi a rayuwar
jama’a da xai xai ku, sai kuma wasiqar maida
martini ga “yan komai daga yanayine, sai
kuma tausassan wasiqu kan qawaye a lahira da
bayanin muhimmancin hijabi, sai saqo zuwa ga
marasa lafiya, da waxanda Allah ya jarrabesu
da wani abu, sai saqo zuwa ga tsofaffi daga
cikin rayuwar mawallafin shi kansa. Da kuma
saqo kan tuni da yake qudundune da imani,
daga qarshe kuma sai saqo kan sunan Allah
mafi girma wato (Ismullahil’A’azam) wanda
ya haxa da “Al’adlu”, “Al fard”, “Al hayyu” da
“Al qayyum”, “Al quddus”.
Mujalladi Na Huxu: Asshu’a’aat
Wannan ya qunshi saqonni guda 15
ne kuma yana farawa da bayani kan cewa
kyawun halittu da xaukaka xan adam suna
29
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
bayyanane tare da tauhidi wato kaxaita Allah
sai risalar (munajati) cikin yawo tsakanin
halittu, sai wasiqar dake cewa mafaka
na daga cikin kulawar Allah qarqashin
﴾Ø × Ö Õ ﴿ da kuma bayanin
alamomin tashin alqiyama, da siffofin shaixan,
da kuma nazari cikin ma’nonin (Attahiyatu
lillahi) wato tahiya. Sai kuma saqonni masu
muhimmanci cikin nazari kan halittu, da
kuma bayani kan cewa imani da ranar qarshe
shine tushen rayuwar jama’a da xai xai ku,
sai muhimmancin imani da mala’iku. Daga
nan kuma sai bayanin xaukaka qara zuwa
kotun Denizli da Afyon wanda Ustaz Nursi
da xalibansa sukayi. Sai kuma saqonni masu
kwantar da hankula waxanda ya aiko lokacin
yana kurkuku. Daga qarshe kuma ya kafa
qwararan hujjoji kan kaxaitakar Allah da
ingancin aike.
Mujalladi Nabiyar: (Isharatul I’jaz Fi
Mazannil Iijaaz)
Malam ya wallafa wannan tafsiri mai
qimane cikin harshen larabci, wanda ya fassara
alhamdu da kuma ayoyi talatin daga cikin
suratul baqara, yana mai bayanin kaiwar qur’ani
matuqa ta yanayin tsarin zubinsa cikin bayani
ma daidaici, wato ta irin da cewar kowace aya
da “yar uwarta, da dacewar jimloli sashe bisa
30
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
sashe, tare da yadda kowane harafi da kowace
jumla suke bada ma’ana. Malam ya fitar da
wannanne duka bisa dogaro da ilimin Balaga,
Nahw, Sarf, da kuma dokokin ilimin Manxiq
da gundarin Usuluddin, da kuma sauran wasu
ilmomi da suke da alaqa da wannan.
Wannan mawallafi yayi shiftar wannan
tafsirine a lokacin da ake kan ruguntsimin yaqin
duniya na farko tsakanin artasai,wanda hakan
bai dakatar dashi ko yarage kaifin fikrarsaba,
wajain shige da fice cikin ma’anonin Alqur’ani
mai girma.
An xanfara (Qalu Anil Qur’an) na farfesa
Imaduddeen Khalil zuwa ga wannan tafsiri.
Mujalladi Na Shida: Al Munthawee Al’arabi
Annuri
Wannan sashe yana qunshe da saqonni
guda shabiyu cikin harshen larabci ga kanunsu
kamar haka:Lama’atun Minattauhidil Haqiqi.
Rashahatun min ma’arifatinnabi s.a.w
La siyyama (fi isbatil hashri).
Qaxratun min bahrittahidi wa zailuha.
Hubabun minumanil qu’ani wa zailuha.
Habbatun min nawatati samaratin min
samaratijinanil Qur’ani wa zailuha.
Zahratun Min Riyadil Qur’anil Hakeem wa
zailuha.
31
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Zarratun min shu’a’I hidayatil Qur’ani wa
zailuha.
Shammatun min nasimil Qur’ani wa zailuha.
Shu’ulatun min anwari shamsil Qur’an.
Nuqxatun min nuri ma’arifatillahi jalla
jalaluhu (fassara).
Nurun min anwari nujumil Qur’an.
Waxannan saqonni gaba xayansu suna
bayanine game da rabe-raben rayuka masu
umarni da mummunan aiki sannan suna
bayyana maganinsu da sauran cututtukan rai,
kuma suna kama hannuun mutane zuwa ga
mavuvvugar imani don zuciya da hankali su
kwankwaxa, ruhi kuma ya samu walwala da jin
daxi.
Wannan gaba xaya bayan tushen fikrar
Ustaz Nursi da zasu kai mutumne, wanda hakan
zai kaishi zuwa fahimtar sha’anin rayuwa
tsakanin halittu, kamar yadda yayi amfani da
hankalinsa cikin ma’aunin ilimi. To wannan
littafi daya ke xauke da Rasa’ilunnur ya tattara
tunanin Sa’id annursine gabaxaya ko ace mafi
kyawun tunaninsa yana cikinsu; domin kuwa
a cikinsune ya sanyawa duk wani musulmi
kai duk wani xan Adam wata sabuwar hanya
ta tsarkake zuciya da kuma tarbiyya. Wanda
samun irinsu a waxansu littafai yayi qaranci
qwarai; sabo dashi yana gwama ma’nonin
32
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
hankaline da kuma shauqin zuciya gami da mafi
hasken abin da ruhi yake fitarwa , cikin misalai
varo-varo. Sannan ya kama hannun mutum
zuwa cikin halin rai yana mai nuna masa halin
rai cikin sauqi , daxi da abinda zai nuna masa
daga abubuwan da ya riska bisa yaqini shi da
kansa, bayan kutsawa da yayi cikin koyarwar
Alqur’ani mai girma.
Mujalladi Na Bakwai: Fi Fiqhi Da’a
Watinnur
Waxannan wasu tarun rubuce-rubucene
waxanda suka gudana tsakanin Ustaz Nursi da
almajiransa na farko, kuma waxannan rubucerubuce suna nusarwane zuwa ga muhimmancin
Rasa’ilunnur da kuma irin salon da suka xauka
wajan kira zuwa ga Allah a wannan zamani,
acikin xaliban akwai waxanda suka bayyana
irin tasirin da Rasa’ilunnur suka musu, da
kuma irin amfanuwa da sukayi dasu, da kuma
irin yanda suka canzamusu rayuwa, suka buxa
musu hanya faffaxa ta ilimi. Bayan haka suna
qara nusarwa zuwa ga kyautata hali da hulxa,
da kuma kwaxaitarwa zuwa ga imani mai zurfi,
da kuma aiki mai xorewa, da riqo da Alqur’ani
da hadisi, da yawaita bauta, addu’a, zikiri da
kyawawan tunani da yawaita tuba, da qasqantar
da kai gaban Allah… da kuma makamantan
waxannan abubuwa da suka shafi duk wani mai
kira zuwa ga Allah, kai! kowanne musulmi a
bayan qasa.
33
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
Abubuwan da aka kara a jikin wannan
mujalladi suna xauke da litattafai guda uku,
kowanne yana cin gashin kansa sune kamar
haka:Mulhaq Barla.
Mulhaq Qasxamoni
Mulhaq Amirdag
Kowanne daga cikinsu yana bayyana wani
matakine na musamman daga matakan rayuwa
Al-Ustaz Nursi, kamar yadda yake bayani kan
matakan da kiran Rasa’ilunnur suka xauka a
qasar Toki; sabo dasu (Almalahiq) sun kasance
suna da wani tsari na musamman wajan kira
zuwa ga musulunci, da kuma yimasa katangar
qarfe daga waxansu munanan abubuwa.
Wannan ko ya kasance tun lokacin da al’ummar
toki suka shiga wani hali na qaqani-kayine
a dalilin siyasa, da hanasu yaxa manufofin
musulunci lokacin da ya rasa mai yimasa
hidima.
Mujalladi Na Takwas: Sayqalul Islam
(Asaru Sa’id Alqadim)
Wannan ya qunshi saqonni kamar haka:Muhakamat aqliyya fit tafsiri wal balagati
wal aqida. (fassara da tabbatarwa) wato amfani
da hankali cikin tafsiri, balaga da kuma aqida.
Qazlu iijaz: hashiyar da Ustaz Nursi yayi
wa (assullamul munauraq) littafin da sheikhul
34
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
islam Abdurrahman Al’akdari ya wallafa kan
ilimin manxiq cikin tsarin waqe, tare da sharhin
Almala Abdulmajid.
Ta’aliqat Ala Burhanil Kalanbawee: shima
risalace a ilimin manxiq, wacce take xauke da
tsokaci da ustaz nursi yayiwa littafin (Alburhan)
na malam Isma’il bin Musxafa Al kalanbawee.
Waxannan wasiqu guda biyu wato “Qazlu
iijaz” da “Ta’aliqat Ala Burhanil Kalanbawee”
ya wallafasune cikin harshen larabci.
Assanihat
Almunazarat
Waxannan wasu wasiqune guda biyu
cikin yaren Toki, suna bada haskene kan
zamantakewa da siyasa kafin yaqin duniya na
farko.
An wallafasune a lokacinda daular
usmaniyya ta shiga wani yanayin data samu
kanta cikin qunci, a saboda da waxannan
wasiqu aka sami warakar waxannan matsaloli.
Almktubatul askariyyatul urfiyya:
Wannan yana bayanine kan tsayuwar
ustaz nursi a gaban kotun soji don kare kansa
a zamanin ittihadiyyun, ana kiran kotun da
(shahadatu madrasatayil musiba); saboda tun
lokacin daya nemi gyara tsarin karatu, da kafa
jami’a mai suna madrasatuzzahra aka kaishi
35
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
asibitin mahaukata, daganan aka kamashi aka
kaishi kotun sojoji aka tuhumeshi da niyyar
maido da shari’a.
Alkuxbatus shamiyya: Itace kuxubar daya
gabatar a sham, yana mai bayani kan ciwon
al’umma da maganinsa a ciki.
Alkhuxwatus situ: An wallafasune sabi da
mamayar da ingila sukaiwa Istanbul, suna qarar
da gwarazansu, suna takwaikwaye himmar
musulmai a wancan lokaci.
Mujalladi Na Tara: Siratun Zatiyya
Yana bayani kan tarihin rayuwar
Badi’uzzaman Sa’id Annursi daki-daki wanda
aka ciro daga cikin rubuce- rubucensa.
Mujalladi Na Goma: Alfaharis (Abin Dake
Ciki) Wanda Ya Rubuta: Hazim Nazim Fadil
36
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
KALMAR FARKO
(Bismillahi)
qashin
bayan
kowane
alheri, kuma farkon kowane al’amari mai
mahimmanci, da ita muma muke farawa.
Yakai rai ka sani cewa wannan kyakkyawar
kalma mai albarka, kamar yadda ta kasance
tambarin musulunci hakanan ita furucin
halittune da qarshen halayensu.
Idan kana kwaxayin sanin abin dake cikin
(Bismillah) nadaga qarfi wanda baya raunana,
da kuma abinda ke cikinta na albarka wanda
baya qarewa to ka saurari wannan taqaitacciyar
hikaya:
Lallai xan qauye wanda yake yawo cikin
sahara don buxe ido, ba makawa sai ya kasance
yana qarqashin sarkin wata qabila, cikin
kulawar wannan sarki, saboda ya kuvuta daga
sharrin maqiya har zuwa ga cimma burinsa,
idan ko bahakaba zai tabbata cikin ximuwa
da rashi kwanciyar hankali shi kaxai, saboda
magauta da kuma buqatu marasa iyaka.
Hakanan… wannan yayi dai-dai da wasu
mutane guda biyu sun fita cikin wannan yawon
bude ido cikin sahara, xaya daga cikinsu ya
kasance mai qasqantar da kai, shiko xayan ya
kasance mai jiji da kai, amma wanda yake mai
qasqantar da kai xin ya kasance qarqashin wani
sarki, shiko wanda yake mai jiji da kai yaqi ya
37
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
kasance a qarqashi kowane sarki, sun kutsa
cikin sahara, da zarar wanda yake qarqashin
wannan sarki ya dumfaro wuri za’a tarveshi
cikin girmamawa idanko ya cikaro da masu
tsaron hanya sai ya cemusu ni ina zagawane da
sunan sarki, sai ya kuvuta daga hannun mugu,
shiko wanda yake mai jiji da kai ya haxu da
masifu iri-iri, da narko daban-daban wanda yafi
qarfin a siffanta tunda duk tsawon tafiyar ya
kasancene cikin tsoro da firgici da kuma saqesaqen zuci, take ya walaqantar da kansa.
To! yakai ruxaxxen rai, kasani cewa kaine
wannan xan qauye da yake yawon buxe ido,
wannan duniya mai faxi kuwa itace wannan
sahara, kuma lallai (talaucinka) da (gazawarka)
basu da iyaka kamar yadda maqiyanki da
buqatunki basu da qarshe to idanko hakane
ka riqi sunan mamallakin wannan sahara na
haqiqa mai iko akanta na har abada, saboda
ka kubuta daga qasqakancin saqe-saqen zuci a
gaban halittu da kuma kubuta daga tozartarwar
tsoro a gaban fararru.
Hakane, lallai wannan kalma mai tsarki
(Bismillahi) taskace mai girma wacce bata
qarewa, tunda dai da itane talauci yake zama
wadata mai faxi fiye da halittu, kuma gazawa
ta rataya da wani iko mai girma wanda zaka
iya riqe ragamar samammu dashi tun daga
38
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
kan zarra zuwa sama .har a wayi gari wannan
talauci da gazawa sun zamo karvavvu a wurin
mai cikakken iko ma’abocin girma da buwaya.
Lallai duk abin da yake motsawa ko yake
shiru kokuma yake wayar gari ko ya maraita
da wannan kalmar (Bismillahi) kamar wanda
ya xaura xamarane ya juya al’mura da sunan
qasa ba tare da yana tsoron kowaba, ta yanda
yana maganane da sunan dokar kasa, sai ya
aiwatar da ayyuka kuma anajinsa a ko’ina . mun
ambata abaya cewa dukkan halitta suna cewa
Bismillahi da harshen halinsu shin hakane?
Hakane, kamar yadda idan kaga mutum
ya xebi mutane zuwa waje guda kuma ya
umarcesu da wasu ayyuka daban-daban, zaka
tabbatar da cewa wannan mutum yana gudanar
da wannan aikine da karfin wani soja wanda
yana qarqashin ikon wani shugaba
To duk waxansu samammu suna gudanar
da ayyukansune qarqashin sunan Allah, to
qwayoyi waxanda suka kai wajan kankanta
suna xauke da bishiyoyi manya-manya a
cikinsu da sunan Allah wato kowacce tana
cewa bismillahi sai ta cika hannunta da amfani
daga cikin taskar Allah sannan ta miqomana,
sanna kowane lambu yana cewa bismillahi
sai ya wayi gari wata tukunyace ta ikon
Allah wacce nau’i-nau’in abinci mai daxi ke
39
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
dafuwa a cikinta, sannan kowace dabba mai
mahimmanci da albarka suna cewa bismillahi,
sai su wayi gari wata mavuvvugace ta madara
sannan su gabatarmana da ita da sunan Allah
da ikon Allah cikin hali mafi tsafta. Hakanan
tushen kowane tsiro yana cewa Bismillahi
saboda haka sai wuri mai tsandauri ya tsage da
ikon Allah wato wannan tsiro ya tsagashi da
tofonsa mai taushi sai ya zama kenan yana da
iko kan abu mai wahala da kuma tsauri.
Qwarai, lallai kaxawar rassa cikin iska da
kuma yadda suke xauke da abin amfani, da kuma
yadda jijiyar tsirrai take ratsa duwarwatsu, da
yadda suke adana abinci cikin kasa… hakanan
yadda korran ganye suke jure zafin rana duk
kaifinta da yadda waxannan rassa suketabbata
cikin damshi da yabanya, wannan gabaxaya
yana rushe ra’ayin waxanda sukayi imani
da samuwar madda kawai wato (maddiyun),
sannan yana nuna musu cewa wannan abu da
suke xagawa da shi cewa zafi da tsandauri
suna aikine da karan kansu to sunayin aikine
da umarni, tayanda waxannan tsirrai suke aiki
kamar sandar annabi Musa wajan fasa tsandauri
da kuma yadda take karvar umarni cikin ayar:
﴾ R Q P O ﴿ wato: (sai mukace
bugi dutsen da sandarka) surat:Baqara, aya:60
yanayin da waxannan ganyayyaki kuma suke
40
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
kamar gavovin annabi Ibrahim a.s wajan rashin
cutuwa daga harshen wuta ﴾ « ª © ¨ ﴿
(yake wuta kizamo sanyi mai aminci…) surat:
Anbiya, aya: 69.
Tunda dai kowane abu yana faxin ma’anar
bismilla, kuma yana tsakuro ni’imar Allah
ya miqomana da bismillahi, muma sai muce
bismillahi, mu bayar da bismillahi , mu karva
da bismillahi, sannan mu maida hannun
rafkanannu da suke qin bayarwa da bismillahi.
Tambaya: lallai mu muna bayyana
girmamawa ga wanda yake sanadiyyar wata
ni’ima a garemu, to menene kakeganin Allah
ma’abocin waxannan ni’momi da kuma
mamallakinsu na haqiqa yake nema daga
garemu?
Amsa: lallai wannan mai ni’imtarwa na
haqiqa yana neman abubuwa guda uku daga
garemu amatsayin tukuicin waxannan ni’momi
masu tsada, sune:
Zikiri
Godiya
Tunani
To (Bismillahi) a farko itace zikiri,
(Alhamdulillhi a qarshe)
shine godiya,
tsakanin su kuwa shine tunani wato lura da mai
da hankali kan waxannan ni’imomi, da kuma
riskar cewa su waxansu mu’ujizozine na ikonsa
41
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
madafa shixaya tilo da kuma shiriyar rahamarsa
mayalwaciya.. wannan lura itace tunani.
Amma wai shin wanda yake sunbantan qafar
soja wanda yake xan aiki kuma yake gabatar da
kyautar sarki, baiyi wawanci da dolanciba? To
idan kuwa hakane yaya kake ganin wanda yake
yabon hanyoyin da suke kawomasa arziki, yake
kevesu da wani suna na musamman batare da
yayi hakan ga mai azurtawa na haqiqaba! Shin
baka ganin yafi wancan wawanci sau dubu?
To ya kai rai!! Idan bakaso ka kasance
kamar wancan wawa dolo, kana bada da
Bismillahi… ka karva da Bismillahi… ka fara
da Bismillahi… kuma kayi aiki da Bismillahi..
wassalam.
42
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
FA’IDOJI DAGA RASA’ILUNNUR
Rasa’ilunnur wasu qwararan
hujjojine game da Alqur’ani mai girma, da
kuma bayani kan matsayinsa. Rasailunnur wata
walqiyace mai haskawa daga cikin hasken
Alqur’ani, sannan wata kamfatace daga cikin
koginsa kuma wani haskene daga ranarsa, kuma
wata haqiqace daga taskar ilimin haqiqa, haka
kuma wata kwaranyace daga makwaranyarsa.
Lalle Rasa’ilunnur wani tsora taccen
haskene, kuma wata hajace aka ciro daga
ilimin gabaci badaga falsafa ko adabinsuba,
kai! An ciroshinema daga qarqashin al’arshin
Alqur’ani maxaukaki wanda ya gagari gabar da
yamma gaba xaya.
Imani yasamu rauni qwarai da gaske
a cikin wannan zamani mai matuqar
firgitarwa,wanda hakan na wajabtawa kowane
mumini ya mallaki imani mai qarfi don ya iya
fito na fito da ruxin zamani da qarerayinsa. To
Rasa’ilunnur suna bada wannan gudummawa
lokacin da akafi buqata, kuma suna isar da saqo
ta hanyar da kowa da kowa zai gane, sannan
suna tabbatar da zurfafan ma’nonin Alqur’ani
da qarfafan hujjoji.
Ilimin addini shine hasken zuciya, hasken
hankali kuma shine ilimiin zamani, haqiqa
kuma tana bayyanane tsakani a qarqashin
Lalle
43
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
cakuxuwa sai himmar xalibi ta hauhawa,
rabasu kuma shike haifar “yan ubanci kan
ilimin addini ya kuma sanya kokwanto cikin
ilinim zamani.
Ya zama dole akan kowane musulmi ya
xaukaka Kalmar Allah, mafi girman hanya
wajan gudanar da wannan aiki itace kece raini,
don waxanda ba musulmaiba, suna tattakamune
sakamakon ilimi da qere-qere da suka fimune.
To muma ya zama dole mu yaqi talauci da
jahilci da kuma savani, wanda savanin hakan
shine maqiyi na farko da yake gaba da xaukaka
Kalmar Allah.
Jahilci, lalura, da savani sune matsalarmu
ta qarshe, to ya zama dole mu yaqesu da
makamin sana’a, ilimi da haxin kai.
Abisa ma’aunin addini, mutanen madina
sun karvi addinine saboda gamsuwa da
sukayi dashi, bada tilastawaba, wanda hakan
yafaru sakamakon nunamusu xaukakarsa da
soyuwarsa a wurunsu ta hanyar kyakkyawan
bin umumninsa da nuna kyawawan tanadi.
Amma tilastawa da gaba kuma su tafarkin yan
tada zaune tsayene.
Buwayar musulunci wacce take xaukaka
Kalmar Allah a wannan zamani tana samuwane
a lokacin da musulunci ya samu cigaba na
zamani, kuma babu kokwanto cewa haqiqar
44
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
duniyar musulunci zata tabbatane qarqashin
cikar imani wanda shine garkuwa ga
musluncin…
Yanke qauna wani ciwone mai kusan
kama da kansa… ga al’umma, kuma shine
yake hanasu cigaba, kamar yadda ya sava da
hadisul qudsi da yake ceewa (ana inda zanni
abdee bee) wato Allah yace ina inda bawana
yake tsammanina… yanke qauna xabi’ar
matsoratane, gajiyayyu da kuma maqasqanta,
amma ba sha’anin jarumta a musulunci bane
ko kaxan… kuma yanke qauna ba xabi’ace
kyakkyawa awurin larabawa na qwaraibane,
wanda kyawawan tanadodi sune abin alfaharin
mutum. Su kuma duniya ta sansu da kafewa da
kuma jajircewa.
Savanin tunani ya jijjiga tushen koyarwar
musulmi qwarai da gaske, kuma ya sanya
rarrbuwar kan al’umma kuma ya daqusar damu
daga hawa dokin wayewa; domin zakaga xaya
na kafirta xaya yana cewa vataccene, alokacin
da zakaga wannan yana ganin wancan jahiline
ba’a yarda da shiba, wannan yasa wuce gona da
iri da kuma gazawa suka mamayemu. Maganin
wannan ciwo kuwa shine sulhu tundaga kan
xayanta tunani, da kuma qulla alaqa wacce zata
kai ga daidaito har kowa ya yarda da juna da
haxin kai don samun cigaba mai xorewa.
Kyakkyawan aiki mai amfani, shine
45
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
aikin da mutum zaiyi daidai da soyayyarsa
ga tafarkinsa kaxai, batare da an maida
tunaninsaba, ko ya sanya gaba da wasu a cikin
iliminsa ko kuma rena sha’aninsu, wato kada
ma ya damu dasu tun farko.
Sai riqo da kundin adalci a matsayin dalili
kuma jagora, shine kowane ma’abocin wata
hanya ta gaskya zai iya cewa: “ lalle tafarkina
gaskiyane, kuma shine yafi” ba tare da yayi
katsalandan a cikin tafarkin wasuba, amma bai
hallata yace: “tafarkinane kawai gaskiyaba”
ko “tafarkinane kaxai yake da kyauba” wanda
haka na nufin munin wasu hanyoyi da varnarsu.
Lokaci mai zuwa na musulunci shi kaxai,
hukunci zai dawo saida qur’ni da imani; sabo
da haka ya zama dole mu yarda da kaddara da
abin da Allah ya tsagamana; tunda dai muna da
qarshe mai kyau, bare kuma sunada rikirkitatten
baya.
Da ace zamu bayyana kyawawan
tanadodin musulunci a cikin ayyukanmu da
tafiyarmu, da waxanda suke bin waxansu
addinai sun shigo musulunci tawaga-tawaga,
kai! Da duk qasashen duniyama sai sun dawo
qarqashin tutar musulunci.
46
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
KULLIYYATU RASA’ILUNNUR A
DUNQULE
Al Kalimat
Al Maktubat
Al Lama’at
Asshu’a’at
Isharatul’I’jaz Fi Mazannil iijaaz
Al Munthawee Al ’Arabee Annuree
Al Malahiq (Fi Fiqh Da’awatinnur)
Saiqalul Islam (Asaru Sa’id Al Qadeem)
Siratun Zatiyya
Al Faharis (Tahliliyyun Am li Rasa’ilinnur)
Majmu’atu Asa Musa
Majmu’atu Zulfiqar
Majmu’atu Sirujunnur
Majmu’atu Asrarun Qur’aniyya
Majmu’atu Almuwazanat Bainal Imani Wal Kufr
47
A Guide For Youth
•
The Short Words
•
Resurrection And Hereafter
•
Belief And Man
•
Thirty Three Windows
•
The Suprime Sign
•
The Fruits of Belief
•
On Ramadan, Thanks and Frugality
•
Sincerity And Brotherhood
•
Nature Cause or Effect
•
A Guide For Women
•
Message For The Sick
•
The Damascus Sermon
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
•
48
RASA’ILINNUR SUNA KAN IDON DUNIYA
www.sozler.com.tr
www.envarnesriyat.com
www.nesil.com.tr
www.iikv.org
www.nur.gen.tr
www.nurnetwork.org
www.nuronline.com
www.nursistudies.com
www.rejhan.net
www.risalahnur.com
www.malaysianur.com
www.nurpublishers.com
www.questionsonislam.com
www.laluzdelafe.org

Benzer belgeler

DE SCRIPT (TURKSE VERSIE)

DE SCRIPT (TURKSE VERSIE) Su benim kizim varya, gercek bir Hollandali gibi. Nerde, nezaman indirim var, herseyi bilir! (Kadin kizi kucakliyor) KIZI Ya ben o kadini hala anliyamadim. Hele o suratsiz hali, bana tuhaf tuhaf ba...

Detaylı

Tayaka murnar sayan Sony Ericsson W760i. Siririyar waya mai salo

Tayaka murnar sayan Sony Ericsson W760i. Siririyar waya mai salo da babukan garanti mai iyaka kafin amfani da wayarka. Wayarka ta hannu tana da damar saukewa, ajiyewa da tura žarin abun ciki, misali, sautunan ringi. Ana iya žuntata ko haramta amfanin irin wannan...

Detaylı

hukunce-hukuncen sallar ıdı

hukunce-hukuncen sallar ıdı haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na SALLAR IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abi...

Detaylı

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa: (3

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa: (3 Sarki ya haramta kisa haka kawai ba tare da dalili na shara'a ba, kuma Ya sanya nau'ukan narkon azaba ga dukkan wannada ya aikata kisa. Karkasuwar Kisankai: Kashi na Farko: Mutum Ya Kashe Kanshi Da...

Detaylı